4 Agusta 2020 - 12:12
Trump Ya Haramta Wa Gwamnati Daukar Ma’aikata 'Yan Waje

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a kan wata doka da ta haramtawa ma’aikatun gwamnatin tarayya daukar ma’aikata daga kasashen waje muddin dai zasu yi ayyukan da Amurka ke yi.

ABNA: Fadar White House ta ce dokar umarnin shugaban kasar zata taimaka wurin haramtawa ma’aikatun gwamnati maye gurbin Amurkawa ma’aikata ba bisa ka’ida ba da ‘yan kasar waje don neman rahusa.

Dokar ta bukaci duk ma’aikatun gwamnati su kamala bincike su nuna ko suna daukar ‘yan asalin Amurka da ‘yan kasa aiki a kan mukaman aiki da mutane da dama ke nema.

Trump ya fadawa manema labarai a jiya Litnin cewa zai kori shugaban ma’aikatar TVA saboda yana daukar ‘yan kasar waje kuma yana daukar albashi mai yawa.

342/